5 Satumba 2021 - 10:06
Najeriya: Hukumar NCC Za Ta Yanke Layukan Sadarwa A Jihar Zamfara

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar Sadarwa ta NCC ta Nigeria ta umurci kamfanonin sadarwa a kasar da su yanke dukkan layukan sadarwa na Jihar Zamfara na tsawon kwanaki biyu a wani yunkuri da ake yi na kawo karshen barazanar hare-haren yan bindigan Daji a fadin jihar da ma Makwabta,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Takardar wadda babban sakataren hukumar ta NCC Farfesa Umar Dambatta ya sanyawa hannu, an bukaci kamfanonin da su gaggauta daukar wannan mataki domin taimakawa jami’an tsaro na ganin an cimma nasara wajen kawo karshen matsalar tsaro da ake fuskanta a yankin.

Wadannan mataken suna zuwa ne A daidai lokacin da gwamnonin jihohin Kaduna, zamfara, Nigeria, Katsina, Niger suka fitar da sabbin dokoki da ya hada da rufe kasuwanni da sauransu a kokarin da suka yi na ganin an dakile hare-haren da yan bindigan dajin suke kaiwa a wadannan jihohi.

342/